1 Thessalonians 5

1Yanzu fa game da zancen lokatai da zamanai ‘yan’uwa, ba ku da bukatar a rubuta maku wani abu. 2Domin ku da kanku kun sani kwarai cewa ranar zuwan Ubangiji kamar barawo take da dare. 3Da suna zancen “zaman lafiya da kwanciyar rai,” sai hallaka ta zo masu ba zato ba tsammani. Zai zama kamar nakudar haihuwa ce da ke kama mace mai ciki. Ba su kwa da wata hanyar kubuta.

4Amma ku, ‘yan’uwa, ai ba cikin duhu kuke ba har da wannan rana zata mamaye ku kamar barawo. 5Domin dukkan ku ‘ya’yan haske ne ‘ya’yan rana kuwa. Mu ba ‘ya’yan dare ba ne ko na duhu, 6Don haka, kada muyi barci kamar yadda sauran ke yi. Maimakon haka, bari mu kasance muna zaman tsaro kuma muna a fadake. 7Don masu yin barci da dare suke yin barci, haka kuma masu sha su bugu ma da dare suke yi.

8Tunda shike mu ‘ya’yan rana ne, bari mu zauna a natse. Bari musa sulke na bangaskiya da kauna, mu kuma sa kwalkwali don ceton mu dake gaba. 9Domin Allah bai kaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijin mu Yesu Almasihu. 10Shi ne wanda ya mutu domin mu, don ko da muna raye ko muna mace, mu iya rayuwa tare da shi, 11Domin haka ku ta’azantar da juna ku kuma inganta juna, kamar yadda kuke yi.

12Muna rokon ku, ‘yan’uwa, ku bada daraja ga wadanda suke aiki a tsakaninku wadanda kuma suke shugabanci a kan ku cikin Ubangiji, wadanda kuma suke horonku. 13Muna kuma rokon ku, da ku kula dasu ku kuma kaunacesu sabili da irin ayyukansu. Ku kuma yi zaman lafiya da junan ku. 14Muna yi maku gargadi ‘yan’uwa; ku jawa marassa ji kunne, ku karfafa marassa karfin zuciya, ku taimaki gajiyayyu, kuyi zaman hakuri da kowa.

15Ku lura kada wani ya rama mugunta da mugunta, Maimakon haka ma, Ku cigaba da abinda ke mai kyau ga juna da kowa duka. 16Kuyi farin ciki koyaushe. 17Kuyi addu’a ba fasawa. 18A cikin kome kuyi godiya. Domin wannan ne nufin Allah a cikin Yesu Almasihu game daku.

19Kada ku hana Ruhun Allah aiki a cikin ku. 20Kada ku raina anabce anabce. 21Ku gwada komai. Ku rike abinda ke mai kyau. 22Ku kaucewa duk wani abinda yayi kama da mugunta.

23Bari Allah na salama ya mai da ku cikakun tsarkaka. Bari dukkan ruhun ku, da zuciyar ku, da jikin ku su zama adanannu marassa zargi domin zuwan Ubangijin mu Yesu Almasihu. 24Wanda ya kira ku mai aminci ne, wanda kuma zai aikata.

25Yan’uwa, kuyi addu’a domin mu. 26Ku gaida dukkan yan’uwa da tsattsarkar sumba. 27Ina rokon ku saboda Ubangiji ku karanta wasikar nan ga dukkan ‘yan’uwa. 28Bari alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu shi kasance tareda ku.

Copyright information for HauULB